Tarihin Albani Sokoto

An haifi Umar Yahaya (Albani Sokoto) a unguwar gidan igwai, dake cikin karamar hukimar Sakkwato ta Arewa, Jihar Sakkwato Nigeria. Yayi karatun firameri a makarantar gidan salihu dake a gidan igwai 2000-2006. Daga bisani ya zarce zuwa makarantar sakandaren jika ka dawo ta gidan igwai 2006-2009. Yayi kammala karatun sa a babbar sakandare dake a runjin sambo. 

Bayan haka, Albani Sokoto ya zarce zuwa birnin zaria dake a jihar kadunan Nigeria domin neman ilimin addinin islama. Umar ya samu karantun islama a wata shahararriyar makaranta dake zaria mai sunan misbahu-ddeen islam wanda ke a unguwar cikaji, Sabon Garin Zaria. a yayin da yayi karatu a wajen malamai daban daban, wanda suka hada da malam Kabiru Abdullahi Cikaji (mawallafin littafin haqqul mubin) kuma directan makarantar. Da kuma malam Ahmad Abdullahi Zaria shugaban malaman makarantar, da mataimakin sa malam Aliyu Kabiru Cikaji.

Haka kuma, Umar yayi karatu a wajen malamai daban daban kamar su;

1. Malam Ibrahim Idris

2. Malam ibrahim Shaukani

3. Malam Sani Muchiya

4. Malam Muhammad Burkila

5. Malam Sani Musa Tudun Muntsira

6. Malam Salisu Muhammad Burkila 

7. Malam Yusuf (Mai walda)

8. Malam Yakubu Muchiya

Bugu da kari, Albani Sokoto yayi karatu a guraren malamai da bazasu kasa yawan hamsin ba. Haka kuma Albani Sokoto ya zama headmaster a makarantar Nana Aisha dake Gidan igwai Sokoto.

More from aKomaCancel
Cancel
Cancel